Rabuwata da kai ke da wuya, sai Ruhun Ubangiji ya kai ka wurin da ban sani ba, don haka, in na tafi na faɗa wa Ahab, in bai same ka ba, to, ni zai kashe, ko da yake ni baranka, tun ina saurayi nake tsoron Ubangiji.
A shekara ta takwas ta mulkinsa, a lokacin yana yaro, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma, sha biyu, sai ya fara tsarkake Yahuza da Urushalima daga masujadai, da Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da siffofi na zubi.
Amma wannan bawa, da fitarsa sai ya tarar da wani abokin bautarsa, wanda yake bi dinari ɗari bashi. Ya cafi wuyarsa, ya ce, ‘Biya ni abin da nake binka.’
Domin zai zama mai girma a wurin Ubangiji, Ba kuwa zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Za a cika shi da Ruhu Mai Tsarki Tun yana cikin uwa tasa.
da kuma yadda tun kana ɗan ƙaramin yaro ka san Littattafai masu tsarki, waɗanda suke koya maka hanyar samun ceto ta dalilin bangaskiya ga Almasihu Yesu.
Sai na ji kamar wata murya a tsakiyar rayayyun halittar nan huɗu tana cewa, “Mudun alkama dinari guda, mudu uku na sha'ir dinari guda, sai dai kada ka ɓāta mai da kuma ruwan inabi!”
Ubangiji kuma ya yi ta bayyana a Shilo inda ya bayyana kansa ga Sama'ila, ya kuma yi magana da shi. Duk lokacin da Sama'ila ya yi magana dukan mutanen Isra'ila suna kasa kunne.