Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 20:19 - Littafi Mai Tsarki

19 su bashe shi ga al'ummai, su yi masa ba'a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 za su kuma bashe shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 20:19
30 Iomraidhean Croise  

Mutane ne marasa hankali marasa suna! Aka kore su daga ƙasar.


Suka wahalshe ni, suka yi mini dariya, Suna hararata da ƙiyayya.


Mutanenmu da suka mutu za su sāke rayuwa! Jikunansu za su sāke rayuwa! Dukan waɗanda suke kwance cikin kaburburansu Za su farka, su yi waƙa don farin ciki! Kamar laimar raɓa wanda yake wartsakar da duniya, Haka Ubangiji zai rayar da waɗanda suka daɗe da mutuwa.


Muka raina shi, muka ƙi shi, Ya daure da wahala da raɗaɗi. Ba wanda ya ko dube shi. Muka yi banza da shi kamar shi ba kome ba ne.


Bayan kwana biyu zai rayar da mu. A rana ta uku kuwa zai tashe mu Mu yi zammanmu a gabansa.


Wato, kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗan Mutum zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa.


Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.


za su kuwa kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Sai duk tsananin baƙin ciki ya rufe su.


Sa'an nan ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi a gicciye shi.


suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu.


Waɗansu ma suka fara tattofa masa yau, suka ɗaure masa idanu, suka bubbuge shi, suna ce masa, “Yi annabci!” Dogaran Haikali kuma suka yi ta marinsa.


Da wayewar gari sai manyan firistoci da shugabanni, da malaman Attaura, da dukkan 'yan majalisa suka yi shawara. Sai suka ɗaure Yesu, suka tafi da shi, suka ba da shi ga Bilatus.


Bilatus kuwa da yake yana son ƙayatar da jama'a, ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, ya ba da shi a gicciye shi.


Gama za a bāshe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa yau.


Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba'a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus.


ya kuma ce musu, “Haka yake a rubuce, cewa wajibi ne Almasihu ya sha wuya, a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu,


shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi.


Da ya zo gare mu, ya ɗauki ɗamarar Bulus ya ɗaure kansa sawu da hannu, ya ce, “Ga abin da Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara, su kuma bashe shi ga al'ummai.’ ”


Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al'ummai da jama'ar Isra'ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan