Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 2:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Sa'an nan ya aike su Baitalami, ya ce, “Ku je ku binciko mini ɗan yaron nan sosai. In kun same shi, ku kawo mini labari, don ni ma in je in yi masa sujada.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Sai ya aike su Betlehem ya ce, “Ku je ku binciko a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 2:8
20 Iomraidhean Croise  

Sai Absalom da dukan mutanen Isra'ila suka ce, “Shawarar Hushai Ba'arkite ta fi ta Ahitofel kyau.” Haka Ubangiji ya nufa ya wofintar da kyakkyawar shawarar Ahitofel don ya jawo wa Absalom masifa.


Sai Yezebel ta aike a wurin Iliya ta ce, “Idan gobe war haka, ban kashe ka ba kamar yadda ka karkashe annabawan nan, to, alloli su hukunta ni.”


Hikima, da haziƙanci, da basira, ba kome suke ba gāba da Ubangiji.


Wa ya umarta, abin kuwa ya faru, In ba Ubangiji ne ya umarta ba?


Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,


Sai Hirudus ya kira masanan nan a asirce, ya tabbata daga bakinsu ainihin lokacin da tauraron nan ya bayyana.


Su kuwa da suka ji maganar sarki, sai suka yi tafiyarsu. Ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gabansu, har ya zo ya tsaya bisa inda ɗan yaron nan yake.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan