Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 2:6 - Littafi Mai Tsarki

6 “ ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza, Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba, Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki, Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda, ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba, gama daga cikinki mai mulki zai zo, wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.’”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 2:6
24 Iomraidhean Croise  

Yana riƙe da sandan mulkinsa, Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, Har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jama'o'i.


A dā sa'ad da Saul yake sarautarmu, kai kake bi da Isra'ilawa zuwa yaƙi, kai kake komo da su. Ubangiji kuma ya ce maka, ‘Kai za ka lura da jama'ata Isra'ila, za ka zama sarkinsu.’ ”


da Salma, shi kuwa ya kafa Baitalami, da Haref ɗansa kuma wanda ya kafa Bet-gader.


Ko da yake Yahuza ya rinjayi 'yan'uwansa, har daga gare shi aka sami shugaba, duk da haka matsayin ɗan farin na Yusufu ne.


Mutanen da suke a garuruwan nan, su ma suka komo. Mutanen Baitalami, mutum ɗari da ashirin da uku Mutanen Netofa, mutum hamsin da shida Mutanen Anatot, mutum ɗari da ashirin da takwas Zuriyar Azmawet, mutum arba'in da biyu Zuriyar Kiriyat-yeyarim, da Kefira, da Biyerot, mutum ɗari bakwai da arba'in da uku Zuriyar Rama da Geba, mutum ɗari shida da ashirin da ɗaya Mutanen Mikmash, mutum ɗari da ashirin da biyu Mutanen Betel da Ai, mutum ɗari biyu da ashirin da uku Zuriyar Nebo, mutum hamsin da biyu Zuriyar Magbish, mutum ɗari da hamsin da shida Zuriyar wancan Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254) Zuriyar Harim, mutum ɗari uku da ashirin Zuriyar Lod, da Hadid, da Ono, mutum ɗari bakwai da ashirin da biyar Mutanen Yariko, mutum ɗari uku da arba'in da biyar Zuriyar Senaya, mutum dubu uku da ɗari shida da talatin (3,630).


Zai lura da garkensa kamar yadda makiyayi suke yi, Zai tattara 'yan raguna wuri ɗaya, Zai ɗauke su ya rungume su, A hankali zai bi da iyayensu.


“Baitalami cikin Efrata, Wadda kike 'yar ƙarama a cikin kabilar Yahuza, Amma daga cikinki wani zai fito wanda zai sarauci Isra'ila Wanda asalinsa tun fil azal ne.”


Yakubu zai yi mulki, Zai hallaka waɗanda suka ragu cikin birni.”


Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,


Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa.


Ya sāke faɗa masa, faɗa ta biyu, “Bitrus ɗan Yahaya, kana ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka kiyaye tumakina.”


Nassi ba cewa ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami yake, ƙauyen da Dawuda ya zauna?”


Allah kuma ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikon Almasihu, ya kuma ba da shi ga Ikkilisiya ya zama Kai mai mallakar abu duka.


Shi ne kai ga jikin nan, wato Ikilisiya. Shi ne tushe, na farko a cikin masu tashi daga matattu, domin ta wurin kowane abu ya zama shi ne mafifici.


Tabbatacce ne, cewa Ubangijinmu ya fito daga zuriyar Yahuza ne, Musa kuwa bai ce kome ba a game da kabilar nan a kan zancen firistoci.


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


zai kuwa mallake su da sanda ta ƙarfe, ya farfashe su kamar tukwanen yumɓu


domin Ɗan Ragon nan da yake a tsakiyar kursiyin, shi zai zama makiyayinsu, zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai. Allah kuma zai share musu dukan hawaye.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan