Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 2:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Sai ya tara dukan manyan firistoci da malaman Attaura na jama'a, ya tambaye su inda za a haifi Almasihu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 2:4
30 Iomraidhean Croise  

Su ne shugabannin masu ɗaukar kaya, suke kuma nuna wa kowane ma'aikaci irin aikin da zai yi, waɗansu daga cikin Lawiyawa, magatakarda ne, da ma'aikatan hukuma, da masu tsaron ƙofofi.


Sai Hilkiya ya ce wa magatakarda Shafan, “Na gāno Littafin Shari'a a Haikalin Ubangiji.” Sai Hilkiya ya ba Shafan littafin.


Dukan manyan firistoci da sauran jama'a gaba ɗaya, sun zama marasa aminci ƙwarai suna aikata dukan abubuwan banƙyama da al'ummai suke yi. Suka ƙazantar da Haikalin Ubangiji wanda ya tsarkake a Urushalima.


Ezra kuwa ya tashi, ya sa firistoci da suke shugabanni, da Lawiyawa, da dukan mutanen Isra'ila su rantse, cewa za su yi abin da aka ce. Sai suka yi rantsuwar.


Ezra ɗin ya taho daga Babila. Shi malami ne, masanin shari'ar Musa, wadda Ubangiji Allah na Isra'ila ya bayar. Sarki kuwa ya ba shi dukan abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.


Sarakunan duniya sun yi tayarwa, Masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare, Gāba da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa.


Ƙaƙa za ku ce, “Muna da hikima, Dokar Ubangiji tana tare da mu”? Ga shi kuwa, alkalamin ƙarya na magatakarda, ya yi ƙarya.


Gama ya kamata bakin firist ya kiyaye ilimi, wajibi ne firistoci su koyar da ilimin gaskiya na Allah, a gare su mutane za su tafi su koyi nufina, domin su manzannina ne, ni Ubangiji Mai Runduna.


Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida yake, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”


Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima.


Sai suka ce masa, “A Baitalami ne, ta ƙasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta cewa,


Amma manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al'ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi.


Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?”


Sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka taru a gidan babban firist, mai suna Kayafa.


Kafin ya rufe baki ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci da shugabanni ne suka turo su.


Da gari ya waye sai duk manyan firistoci da shugabannin jama'a suka yi shawara a kan Yesu su kashe shi.


domin yana koya musu da hakikancewa, ba kamar malamansu na Attaura ba.


Ya fara koya musu, cewa lalle ne Ɗan Mutum ya sha wuya iri iri, shugabanni, da manyan firistoci, da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi da rai.


Nan take malaman Attaura da manyan firistoci suka nema su kama Yesu, don sun lura a kansu ne ya ba da misalin, amma suna jin tsoron jama'a.


Manyan firistoci da malaman Attaura na nan a tsaitsaye, suna tsananta kai ƙararrakinsa ainun.


Yahuza kuwa bayan ya ɗauko ƙungiyar soja, da waɗansu dogaran Haikali daga manyan firistoci da Farisiyawa, suka zo wurin, riƙe da fitilu, da jiniyoyi, da makamai,


Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai ma da kake malamin Isra'ila, ba ka fahimci waɗannan al'amura ba?


Farisiyawa suka ji taro suna raɗeraɗinsa haka, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki dogaran Haikali su kamo shi.


Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka kawo wata mace da aka kama da zina. Da suka tsai da ita a tsaka,


Sai ƙasaitacciyar hargowa ta tashi, waɗansu malamai kuma na ɗariƙar Farisiyawa suka miƙe a tsaye, suka yi ta yin matsananciyar jayayya, suna cewa, “Mu ba mu ga laifin mutumin nan ba. In wani ruhu ne ko mala'ika ya yi masa magana fa?”


Kashegari shugabanninsu da dattawansu da malamansu na Attaura suka taru a Urushalima,


Ta haka suka ta da hankalin jama'a, da shugabanni, da malaman Attaura, su kuma suka aukar masa, suka kama shi, suka kawo shi a gaban majalisa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan