Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 2:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Sai ya je ya zauna a wani gari wai shi Nazarat, domin a cika faɗar annabawa cewa, “Za a kira shi Banazare.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 ya je ya zauna a wani garin da ake kira Nazaret. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa, “Za a ce da shi Banazare.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 2:23
20 Iomraidhean Croise  

Wannan ita ce ka'idar zama keɓaɓɓe a ranar da keɓewarsa ta cika. Za a kai shi ƙofar alfarwa ta sujada,


An yi wannan ne duk, don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa,


Sai jama'a suka ce, “Ai, wannan shi ne Annabi Yesu daga Nazarat ta ƙasar Galili.”


Da ya fito zaure, sai wata baranya kuma ta gan shi, ta ce wa waɗanda suke tsaitsaye a wurin, “Ai, mutumin nan tare yake da Yesu Banazare!”


yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”


Sai ya zamana a wannan lokaci Yesu ya zo daga Nazarat ta ƙasar Galili. Yahaya ya yi masa baftisma a Kogin Urdun.


A wata na shida Allah ya aiko mala'ika Jibra'ilu zuwa wani gari a ƙasar Galili, wai shi Nazarat,


Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne yake wucewa.”


Bayan sun ƙare kome da kome bisa ga Shari'ar Ubangiji, sai suka koma ƙasar Galili suka tafi garinsu Nazarat.


Suka amsa masa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce musu, “Ni ne.” Yahuza kuwa da ya bāshe shi yana tsaye tare da su.


Sai ya sāke tambayarsu, “Wa kuke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.”


Bilatus kuma ya rubuta wata sanarwa, ya kafa ta a kan gicciyen. Abin da aka rubuta ke nan, “Yesu Banazare Sarkin Yahudawa.”


“Ya ku 'yan'uwa, Isra'ilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu'ujizai, da abubuwan al'ajabi, da alamu waɗanda ya yi ta wurinsa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani,


Mun tarar da mutumin nan fitinanne ne, yana ta da hargitsi tsakanin Yahudawa ko'ina a duniya, shi kuma ne turun ɗariƙar Nazarawa.


gama za ki yi juna biyu, ki haifi ɗa. Ba za ki taɓa aske kansa ba Zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki. Shi ne zai ceci Isra'ilawa daga hannun Filistiyawa.”


Ta yi wa'adi, ta ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, idan lalle ka dube ni, ni baiwarka, ka tuna da ni, ba ka manta da ni baiwarka ba, amma ka ba ni ɗa, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji dukan kwanakinsa, aska kuwa ba za ta taɓa kansa ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan