Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 2:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Amma da ya ji Arkilayus ya gāji ubansa Hirudus, yana mulkin ƙasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Amma da aka yi masa gargaɗi a mafarki, sai ya ratse zuwa ƙasar Galili.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wanda ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi a mafarki, sai ya ratse zuwa gundumar Galili,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 2:22
18 Iomraidhean Croise  

Zai kiyaye shigarka da fitarka, Tun daga yanzu har abada.


Cewa wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin, Shi ne zai bishe mu a dukan zamanai masu zuwa.


Shawararka, tana bi da ni, Daga ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja.


Idan kuka kauce daga hanya zuwa dama ko hagu, za ku ji muryarsa a bayanku yana cewa, “Ga hanyan nan, ku bi ta.”


Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne.


Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,


Amma bayan mutuwar Hirudus, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar, ya ce,


Sai ya tashi, ya ɗauki ɗan yaron da uwa tasa, ya zo ƙasar Isra'ila.


A lokacin nan ne Yesu ya zo daga ƙasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma.


Bayan sun ƙare kome da kome bisa ga Shari'ar Ubangiji, sai suka koma ƙasar Galili suka tafi garinsu Nazarat.


Suka amsa masa suka ce, “Kai ma Bagalile ne? Bincika mana ka gani, ai, ba wani annabi da zai bayyana a ƙasar Galili.”


Sama'ila kuwa ya ce, “Ƙaƙa zan yi wannan? Gama idan Saul ya ji zai kashe ni.” Sai Ubangiji ya ce, “Ka tafi da ɗan maraƙi, ka ce, ka zo ne ka miƙa wa Ubangiji hadaya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan