17 A lokacin ne aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa,
17 Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa,
Maganar Irmiya ɗan Hilkiya ke nan, na cikin firistocin da suke a Anatot, a yankin ƙasar Biliyaminu,
ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya faɗa ne ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kirawo Ɗana.”
Da Hirudus ya ga masanan nan sun mai da shi wawa, sai ya hasala ƙwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan nan.
“An ji wata murya a Rama, Ta kuka da baƙin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta. Ba za ta ta'azantu ba, don ba su.”
Ta haka aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa, “Sun ɗauki kuɗin azurfa talatin ɗin nan, wato, awalajar shi wannan da waɗansu Isra'ilawa suka yi wa kima,