Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 2:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Da Hirudus ya ga masanan nan sun mai da shi wawa, sai ya hasala ƙwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan nan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 2:16
21 Iomraidhean Croise  

sai ta yi kira ga mutanen gidan, ta ce musu, “Ku duba ku gani, ya kawo mana Ba'ibrane ya ci mutuncinmu. Ya zo wurina don ya kwana da ni, sai na yi ihu da ƙarfi.


Sai ta mayar masa da magana, ta ce, “Baran nan, Ba'ibrane wanda ka kawo cikinmu, ya shigo wurina don ya ci mutuncina,


La'ananne ne fushinsu domin mai tsanani ne, Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce. Zan warwatsa su cikin dukan ƙasar Yakubu, In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa.


Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?” Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama'ar Isra'ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”


Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu, Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi, Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.


Talakawa ba su da wani taimako sa'ad da suke ƙarƙashin mulkin mugun. Abin tsoro ne shi kamar zaki mai ruri, ko beyar mai sanɗa.


Mutumin da yake da laifin kisankai, yana haƙa wa kansa kabari da gaggawa. Kada ka yi ƙoƙarin hana shi.


Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama'arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.


Kukan sheƙa a guje don ku aikata mugunta, kuna gaggawar zub da jinin marasa laifi. Tunaninku tunanin mugunta ne, lalatarwa da hallakarwa suna a manyan karaukunku.


Nebukadnezzar fa, ya husata ya umarta a kawo Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Sai aka kawo su gaban sarki.


Domin haka hayaniyar yaƙi za ta tashi a tsakanin jama'arku. Dukan kagaranku za a hallaka su. Kamar yadda Shalmanesar ya hallaka Bet-arbel a ranar yaƙi. An fyaɗa uwaye da 'ya'yansu a ƙasa.


Bal'amu ya ce mata, “Domin kin shashantar da ni, da a ce ina da takobi a hannuna, da na kashe ki.”


Sai Balak ya husata da Bal'amu, ya tafa hannunsa ya ce wa Bal'amu, “Na kirawo ka don ka la'anta maƙiyana, amma ga shi, har sau uku kana sa musu albarka.


Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,


A lokacin ne aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa,


Sai Hirudus ya kira masanan nan a asirce, ya tabbata daga bakinsu ainihin lokacin da tauraron nan ya bayyana.


Wutsiyarsa ta sharo sulusin taurari, ta zuba su a ƙasa. Sai macijin ya tsaya a gaban matar nan mai naƙuda, don ya lanƙwame ɗan nata in ta haife shi.


Sai na ga matar ta bugu da jinin tsarkaka, da kuma jinin mashaidan Yesu. Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai da gaske.


Delila kuma ta ce wa Samson, “Ga shi, ka yi mini ba'a, ka ruɗe ni. Ina roƙonka, ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan