Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 2:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron, tare da uwa tasa Maryamu, suka fāɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwar zinariya, da lubban, da mur.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 2:11
33 Iomraidhean Croise  

Mahaifinsu, Isra'ila ya ce musu, “In tilas haka zai zama, sai ku yi wannan, ku ɗiba daga cikin zaɓaɓɓu, mafiya kyau na albarkar ƙasar a cikin tayakanku, ku kai wa mutumin tsaraba, da ɗan man shafawa na ƙanshi da 'yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta, da ɓaure.


Sa'an nan Sarauniyar Sheba ta ba sarki talanti ɗari da ashirin na zinariya, da kayan yaji mai yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa kamar yadda Sarauniyar Sheba ta kawo wa sarki Sulemanu ba.


Ta iso Urushalima da 'yan rakiya da yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya da yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa duk abin da yake a ranta.


Ku yi mubaya'a da Ɗan, Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu, Gama yakan yi fushi da sauri. Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!


Tufafinka suna ƙanshin turaren mur, da na aloyes, da na kashiya, A kowace fādar hauren giwa, mawaƙa suna yi maka waƙar.


Sarakunan Esbanya da na tsibirai, Za su ba shi kyautai, Sarakunan Arabiya da na Habasha Za su kawo masa kyautai.


Ran sarki yă daɗe! Da ma a ba shi zinariya daga Arabiya, Da ma a yi masa addu'a dukan lokaci, Allah ya sa masa albarka kullum!


Ku zo, mu durƙusa, mu yi masa sujada, Mu durƙusa a gaban Ubangiji, Mahaliccinmu!


“Ɗauki kayan yaji masu kyan gaske, ruwan mur na shekel ɗari biyar, da kirfa mai daɗin ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin, da turaren wuta mai ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin,


Ubangiji ya ce wa Musa, “Ɗauki kayan yaji masu ƙanshi, su stakte, da onika, da galbanum tare da lubban. Su zama daidai wa daida.


Wane ne wannan da yake fitowa daga cikin jeji, Kamar tunnuƙewar hayaƙi cike da kayan ƙanshi iri iri na fatake?


Babban ayarin raƙuma zai zo daga Madayana da Efa. Za su zo daga Sheba, su kawo zinariya da kayan ƙanshi. Mutane za su ba da labari mai daɗi a kan abin da Allah ya yi!


Ɗaya daga cikinsu zai ɗibi lallausan garin hadayar wanda aka zuba masa mai da lubban cike da tafin hannunsa. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa.


“Mutane daga kowaɗanne sassa na duniya za su girmama ni. Ko'ina za su ƙona mini halattacciyar hadaya, gama dukansu za su girmama ni,” in ji Ubangiji Mai Runduna.


Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu take. Sa'ad da Yusufu yake tashin Maryamu mahaifiyar Yesu, tun ba a ɗauke ta ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Mai Tsarki.


Yana cikin magana da taro, sai ga Uwa tasa da 'yan'uwansa suna tsaye a waje, suna nema su yi magana da shi.


Na cikin jirgin suka yi masa sujada, suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.”


Da suka ga tauraron sai suka yi matuƙar farin ciki.


“Ina wanda aka haifa Sarkin Yahudawa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo mu yi masa sujada.”


Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamu da Yusufu, da kuma jaririn kwance a komin dabbobi.


Nan take ita ma ta zo, ta yi wa Allah godiya, ta kuma yi maganar ɗan yaron nan ga dukan masu sauraron fansar Urushalima.


Nikodimu kuma, wanda farkon zuwansa wurin Yesu da dad dare ne, ya zo da mur da al'ul a gauraye, wajen awo ɗari.


Sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada, amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka, waɗanda suke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Domin gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.


Da ya ɗauki littafin, rayayyun halittan nan guda huɗu, da dattawan nan ashirin da huɗu, suka fāɗi gaban Ɗan Ragon, kowannensu yana riƙe da molo, da tasar zinariya a cike da turare, waɗanda suke addu'o'in tsarkaka.


Amma waɗansu shashashan mutane suka ce, “Ƙaƙa wannan yaro zai iya cetonmu?” Suka raina shi, ba su kawo masa gaisuwa ba. Amma bai ce kome ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan