Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 2:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 2:1
25 Iomraidhean Croise  

Yankin ƙasar da suka zauna shi ne ya milla tun daga Mesha, har zuwa wajen Sefar, ƙasar tudu ta gabas.


Amma ga 'ya'yan ƙwaraƙwarai Ibrahim ya ba da kyautai, ya sallame su tun yana da rai, su tafi nesa da Ishaku zuwa can cikin ƙasar gabas.


Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir'auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su.


Yana riƙe da sandan mulkinsa, Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, Har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jama'o'i.


Hikimar Sulemanu ta fi ta dukan mutanen gabas, ko masu hikima na Masar.


da Salma, shi kuwa ya kafa Baitalami, da Haref ɗansa kuma wanda ya kafa Bet-gader.


Yana da tumaki dubu bakwai (7,000), da raƙuma dubu uku (3,000), da shanu dubu guda (1,000), da jakuna ɗari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a ƙasar gabas arziki nesa.


Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.


“Baitalami cikin Efrata, Wadda kike 'yar ƙarama a cikin kabilar Yahuza, Amma daga cikinki wani zai fito wanda zai sarauci Isra'ila Wanda asalinsa tun fil azal ne.”


amma bai san ta ba, sai bayan da ta haifi ɗanta, ya kuma sa masa suna Yesu.


Da Hirudus ya ga masanan nan sun mai da shi wawa, sai ya hasala ƙwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan nan.


Amma bayan mutuwar Hirudus, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar, ya ce,


Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima.


Sai suka ce masa, “A Baitalami ne, ta ƙasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta cewa,


Sai Hirudus ya kira masanan nan a asirce, ya tabbata daga bakinsu ainihin lokacin da tauraron nan ya bayyana.


A zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar Abaija. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu.


Domin yau an haifa muku Mai Ceto a birnin Dawuda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji.


Da mala'iku suka tafi daga gare su suka koma Sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu tafi Baitalami yanzu, mu ga abin nan da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar da mu.”


Nassi ba cewa ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami yake, ƙauyen da Dawuda ya zauna?”


Akwai wani saurayi Balawen da yake zama a Baitalami ta Yahudiya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan