Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 19:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Ina kuma gaya muku, kowa ya saki mata tasa, in ba a kan laifin zina ba, ya kuma auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 19:9
18 Iomraidhean Croise  

Amma Allah ya zo wurin Abimelek cikin mafarki da dad dare ya ce masa, “Mutuwa za ka yi saboda matar da ka ɗauko, gama ita matar wani ce.”


A kan wannan kuma, ya yi masujadai a tuddan ƙasar Yahuza, ya sa mutanen Urushalima su zama marasa aminci, ya sa Yahuza ta ratse.


Ubangiji ya ce, “Idan mutum ya saki matarsa, Ta kuwa rabu da shi, har ta auri wani, Ya iya ya komo da ita? Ashe, yin haka ba zai ƙazantar da ƙasar ba? Ya Isra'ila, kin yi karuwanci, Abokan sha'anin karuwancinki, suna da yawa. Za ki sāke komowa wurina? Ni, Ubangiji, na faɗa.


Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra'ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci.


“Amma kin dogara ga kyanki, kika yi karuwanci saboda shahararki. Kin yi ta karuwancinki da kowane mai wucewa.


Kin yawaita karuwancinki da Kaldiya, ƙasar ciniki, duk da haka ba ki ƙoshi ba.


“Sa'ad da na sāke wucewa kusa da ke, na dube ki, ga shi, kin kai lokacin da za a ƙaunace ki, sai na yafe miki tufata, na rufe tsiraincinki, na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, ni Ubangiji Allah na faɗa.


Sai almajiran suka ce masa, “In ko haka tsakanin mutum da mata tasa yake, ashe ma, rashin yin aure ya fi amfani.”


Ya ce musu, “Don taurinkanku ne Musa ya yardar muku ku saki matanku, amma ba haka yake ba tun farko.


Amma ni ina gaya muku, kowa ya saki matarsa, in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta hanyar zina ke nan. Wanda kuma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”


“Kowa ya saki mata tasa ya auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya ya yi zina.”


Ana ta cewa akwai fasikanci a tsakaninku, irin wanda ba a yi ko a cikin al'ummai, har wani yana zama da matar ubansa.


Igiyar aure tana wuyan mace, muddin mijinta yana da rai. In kuwa mijinta ya mutu, to, tana da dama ta auri wanda take so, amma fa, sai mai bin Ubangiji.


Matar kuwa ba ta da iko da jikinta, sai dai mijin, haka kuma mijin ba shi da iko da jikinsa, sai dai matar.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan