Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 19:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ya kuma ce, “Don haka fa sai mutum ya bar uwa tasa da ubansa, ya manne wa mata tasa. Haka su biyun nan su zama jiki guda.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 19:5
19 Iomraidhean Croise  

Ransa kuwa ya zaƙu da son Dinatu 'yar Yakubu. Ya ƙaunaci budurwar, ya kalallame ta da maganganu masu daɗi.


“Na damu ƙwarai saboda kai, ɗan'uwana Jonatan, Ƙaunatacce kake a gare ni! Ƙaunarka a gare ni abar al'ajabi ce, Ta fi ƙaunar mace.


Suna kuwa cikin al'umman da Ubangiji ya umarci jama'ar Isra'ila, ya ce, “Kada ku yi aurayya da su, gama hakika za su karkatar da zuciyarku zuwa gumakansu.” Sulemanu kuwa ya manne wa waɗannan mata da yake ƙauna.


Ki ji abin da zan faɗa, ya ke amaryar sarki, Ki manta da mutanenki da danginki.


Raina yana manne maka, Ikonka yana riƙe da ni.


Ashe, ba kai da ita Allah ya maishe ku jiki ɗaya da ruhu ɗaya ba? Me Allah yake nufi da wannan? Yana so 'ya'yanmu su zama 'yan halal masu tsoron Allah. Domin haka ku kula fa, kada kowa ya ci amanar matarsa ta ƙuruciya.


Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne. Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.”


Ƙauna ta kasance sahihiya. Ku yi ƙyamar abin da yake mugu, ku lazamci abin da yake nagari.


Ashe, ba ku sani ba, duk wanda ya tara da karuwa, sun zama jiki ɗaya ke nan? Domin a rubuce yake cewa, “Su biyun za su zama jiki ɗaya.”


Amma don gudun fasikanci sai kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.


Matar kuwa ba ta da iko da jikinta, sai dai mijin, haka kuma mijin ba shi da iko da jikinsa, sai dai matar.


“Saboda haka ne, mutum sai ya bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya manne wa matarsa, su biyu su zama jiki guda.”


Sai kuma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa. Ku manne masa, ku yi rantsuwa da sunansa.


“Idan dai za ku lura, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda nake umartarku ku kiyaye, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a dukan hanyoyinsa, ku manne masa,


Amma ku da kuka dogara ga Ubangiji Allahnku, a raye kuke har yau.


Da Dawuda ya gama magana da Saul, sai zuciyar Jonatan ta saje da ran Dawuda. Jonatan kuwa ya ƙaunaci Dawuda kamar kansa.


Dawuda kuma ya auro Ahinowam Bayezreyeliya, dukansu biyu kuwa suka zama matansa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan