Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 19:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Amma Yesu ya dube su, ya ce musu, “Ga mutane kam, ba mai yiwuwa ba ne, amma gun Allah kowane abu mai yiwuwa ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 19:26
16 Iomraidhean Croise  

Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji? A ajiyayyen lokaci zan komo wurinka, cikin wata tara, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.”


Garin da yake cikin tukunyar bai ƙare ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya.


“Na sani kai kake da ikon yin dukan abu, Ba wanda ya isa ya hana ka yin abin da ka nufa.


Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji, Bari yă sa wa jama'arsa albarka!


Sau ɗaya Allah ya faɗa, Sau biyu na ji, cewa Allah yake da iko.


“Ya Ubangiji Allah, kai ne ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka da ƙarfinka, ba abin da ya fi ƙarfinka.


“Ni ne Ubangiji Allah na dukan 'yan adam, ba abin da ya fi ƙarfina.


“Idan abin nan ya zama mawuyaci ga sauran jama'a a kwanakin nan, zai zama mawuyacin abu ne a gare ni?


Sai Ubangiji ya amsa wa Musa, “Ikon Ubangiji ya gaza ne? Yanzu za ka gani ko maganata gaskiya ce, ko ba gaskiya ba ce.”


Da almajiran suka ji haka, sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”


Sai Bitrus ya amsa ya ce, “To, ai, ga shi mun bar kome, mun bi ka. Me za mu samu ke nan?”


Yesu ya dube su, ya ce, “Ga mutane kam ba mai yiwuwa ba ne, amma fa ba ga Allah ba. Domin kowane abu mai yiwuwa ne a gun Allah.”


Ba wata faɗar Allah da za ta kasa cika.”


Amma Yesu ya ce, “Abin da ya fi ƙarfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”


sa'an nan kuma suka ridda, ba mai yiwuwa ba ne a sāke jawo su ga tuba, tun da yake sāke gicciye Ɗan Allah suke yi, su da kansu, suka kuma wulakanta shi a sarari.


Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan