Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 19:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Da saurayin nan ya ji haka, sai ya tafi, yana baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 19:22
17 Iomraidhean Croise  

Ka cece ni daga gare su da ikonka, Ka cece ni daga waɗanda suke da duk abin da suke so a duniyan nan, Ka hukunta su da wahalar da ka shirya musu, Ka sa har 'ya'yansu, su ma, ta ishe su, Wahalar da ta ragu kuma, ta sami jikokinsu!


Sukan zo wurinka su zauna, sai ka ce su mutanena ne, sukan ji abin da ka ce, amma ba za su aikata ba, gama suna nuna ƙauna da baka, amma sun ƙwallafa zuciyarsu a kan ƙazamar riba.


Wanda ya faɗa cikin ƙaya kuwa, shi ne wanda ya ji Maganar, amma taraddadin duniya da jarabar dukiya sukan sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.


Sai sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ya yi umarni a ba ta.


Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?


Yesu ya ce masa, “In kana so ka zama kammalalle, sai ka je ka sayar da duk mallakarka, ka bai wa gajiyayyu, ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”


Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Hakika, ina gaya muku, da wuya mai arziki ya sami shiga Mulkin Sama.


“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu; ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”


Da jin wannan magana gabansa ya fāɗi, ya tafi yana baƙin ciki, don yana da arziki ƙwarai.


Sai sarki ya yi baƙin ciki gaya, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ba ya so ya hana ta.


Da jin haka, sai ya yi baƙin ciki gaya, don shi mai arziki ne da gaske.


Lalle hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, amma duniya za ta yi farin ciki. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki.


Kun dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayi (wanda shi da mai bautar gumaka duk ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Almasihu da na Allah.


Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha'awace-sha'wacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha'awa, da mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan