Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 19:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 19:19
15 Iomraidhean Croise  

“Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.


Idan ɗa ya raina mahaifi, ya kuma yi wa mahaifiya ba'a hankakin kwari za su ƙwaƙule masa idanu, 'ya'yan mikiya za su cinye.


Kada ya ɗaukar wa kansa fansa a kan wani ko ya yi ta ƙinsa, amma ya ƙaunaci sauran mutane kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ni ne Ubangiji.


Sai ko wannenku ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya kuma kiyaye lokatan sujada. Ni ne Ubangiji Allahnku.


Saurayin ya ce masa, “Ai, duk na kiyaye waɗannan, me kuma ya rage mini?”


Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’


“Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan'uwanka, ka ƙi magabcinka.’


Sai ya amsa ya ce, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan ƙarfinka, da dukkan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.”


Umarnan nan cewa, “kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi,” da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”


Don duk Shari'a an ƙunshe ta ne a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”


“ ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka domin ka yi tsawon rai, ka sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.


Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan