Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 19:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Sai ya ce masa, “Don me kake tambayata a kan abin da yake nagari? Ai, Managarci ɗaya ne. In kuwa kana so ka sami wannan rai, to, ka kiyaye umarnan nan.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 19:17
14 Iomraidhean Croise  

Ka gargaɗe su su yi biyayya da koyarwarka, Amma sun bijire wa dokoki saboda girmankai, Ko da yake kiyaye dokarka ita ce hanyar rai. Masu taurinkai sun taurare, sun ƙi yin biyayya.


Managarci ne kai, mai alheri ne kuma, Ka koya mini umarnanka!


Me ya sa kake fariya da muguntarka, Ya kai, babban mutum? Ƙaunar Allah tana nan a koyaushe.


“Amma 'ya'yansu suka tayar mini, ba su kiyaye dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka kuma ɓata ranar Asabar ɗina. Sai na yi tunani zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu a jeji.


Domin haka sai ku kiyaye dokokina da ka'idodina waɗanda ta wurin kiyaye su mutum zai rayu. Ni ne Ubangiji.”


Gama Musa ya rubuta zancen adalcin da yake samuwa ta wurin bin Shari'a, cewa mai iya aikata ta zai rayu ta wurinta.


Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.


Mun sani, mun kuma gaskata ƙaunar da Allah yake yi mana. Allah shi ne ƙauna wanda yake a dawwame cikin kauna kuwa, ya dawwama a cikin Allah ke nan, Allah kuma a cikinsa.


“Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji, Babu wani mai kama da shi, Ba mai kiyaye mu kamar Allahnmu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan