Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 18:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 18:6
16 Iomraidhean Croise  

Ya ce, “Kada ku taɓi bayina, zaɓaɓɓu, Kada ku cuci annabawana!”


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Bayan ɗaukaka ya aike ni zuwa wurin al'umman duniyan nan da suka washe ku, gama wanda ya taɓe ku, ya taɓi ƙwayar idona.


Duk da haka, don kada mu ba su haushi, ka je teku ka yi fatsa, kifin da ka fara kamawa kuwa shi za ka ɗauka. In ka buɗe bakinsa za ka sami shekel guda a ciki. To, sai ka ɗauki shekel ɗin nan ka kai musu, wato, nawa da naka.”


“Ku dai lura, kada ku raina ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara. Ina gaya muku, mala'ikunsu a Sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin Sama.


Haka ma, ba nufin Ubanku da yake cikin Sama ba ne ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya hallaka.”


“Wanda duk ya karɓi ƙaramin yaro ɗaya kamar wannan saboda sunana, Ni ya karɓa.


“Da dai wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku.


Shi kuma ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.


Ya kyautu kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa ɗan'uwanku yin tuntuɓe.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan