Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 18:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Da abokan bautarsa suka ga abin da ya faru, suka yi baƙin ciki gaya, har suka je suka gaya wa ubangidansu duk abin da ya gudana.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 18:31
16 Iomraidhean Croise  

Wannan shi ne tarihin zuriyar Yakubu. Yusufu yana da shekara goma sha bakwai sa'ad da ya zama makiyayin garke tare da 'yan'uwansa, ɗan ƙanƙanen yaro ne a tsakanin 'ya'ya maza na Bilha da Zilfa matan mahaifinsa. Sai Yusufu ya kawo labarin munanan abubuwa da 'yan'uwansa suke yi a wurin mahaifinsa.


Hawayena suna malalowa kamar kogi, Saboda jama'a ba su biyayya da shari'arka ba.


Sa'ad da na dubi waɗannan maciya amana, Sai in ji ƙyama ƙwarai, Domin ba su yi biyayya da umarninka ba.


Da ma kaina ruwa ne kundum, Idanuna kuma maɓuɓɓuga ne, Da sai in yi ta kuka dare da rana, Saboda an kashe jama'ata!


Sai sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ya yi umarni a ba ta.


Amma wannan bawa, da fitarsa sai ya tarar da wani abokin bautarsa, wanda yake bi dinari ɗari bashi. Ya cafi wuyarsa, ya ce, ‘Biya ni abin da nake binka.’


Amma ya ƙi, ya kuma je ya sa shi a kurkuku, har yā biya bashin.


Sai ubangiji nasa ya kira shi, ya ce masa, ‘Kai mugun bawa ne! Na yafe maka duk bashin nan saboda ka roƙe ni,


Da ya duddube su da fushi, yana baƙin ciki da taurin zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.


Bawan ya dawo ya ba ubangijinsa labari. Sai maigidan ya yi fushi, ya ce wa bawansa, ‘Fita maza, ka bi titi-titin birni da kwararo-kwararo, ka ɗebo gajiyayyu, da musakai, da makafi, da guragu.’


Da ya matso kusa, ya kuma hangi birnin, sai ya yi masa kuka,


Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.


Mu kam, saboda rauninmu, wane mu da yin haka! Amma ta ko yaya wani yake ƙarfin halin yin fariya, ina magana a kan ni wawa ne fa! to, ni ma sai in yi.


Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku bi umarnansu, don su ne masu kula da rayukanku, su ne kuma za su yi lissafin aikinsu, don su yi haka da farin ciki, ba da baƙin ciki ba, don in sun yi da baƙin ciki ba zai amfane ku ba.


Ku riƙa tunawa da waɗanda suke kurkuku, kamar tare kuke a ɗaure, da kuma waɗanda ake gwada wa wuya, kamar ku ake yi wa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan