30 Amma ya ƙi, ya kuma je ya sa shi a kurkuku, har yā biya bashin.
30 “Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin.
Ku ce musu su jefa wannan mutum a kurkuku, a riƙa ciyar da shi da abinci kaɗan da ruwan sha kaɗan, har na komo lafiya.”
Idan ka ƙi jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba.
Sai abokin bautarsa ya faɗi a gabansa, ya yi ta roƙonsa ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, ai, zan biya ka.’
Da abokan bautarsa suka ga abin da ya faru, suka yi baƙin ciki gaya, har suka je suka gaya wa ubangidansu duk abin da ya gudana.