Suka ƙi yin biyayya, Suka manta da dukan abin da ka yi, Suka manta da al'ajaban da ka aikata. Cikin fāriyarsu suka zaɓi shugaba, Don su koma cikin bauta a Masar. Amma kai Allah ne mai gafartawa, Kai mai alheri ne, mai ƙauna, Jinƙanka da girma yake, ba ka yashe su ba.
“Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu? Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra'ila? Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma? Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim? Zuciyata tana motsawa a cikina, Juyayina ya huru.
Amma wannan bawa, da fitarsa sai ya tarar da wani abokin bautarsa, wanda yake bi dinari ɗari bashi. Ya cafi wuyarsa, ya ce, ‘Biya ni abin da nake binka.’