Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 18:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wanda yake bi talanti dubu goma bashi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 18:24
17 Iomraidhean Croise  

Ya ce, “Bari ya zama kamar yadda kuka faɗa, shi wanda aka sami abin a wurinsa zai zama bawana, sauranku kuwa za ku tafi lafiya.”


Sun ba da zinariya talanti dubu biyar (5,000), da darik dubu goma (10,000), da azurfa talanti dubu goma (10,000), da tagulla talanti goma sha takwas (18,000), da ƙarfe talanti dubu ɗari (100,000).


Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.


Ina nutsewa cikin ambaliyar zunubaina, Ina jin nauyinsu, sun danne ni ƙasa.


Wahalai iri iri sun kewaye ni, har ba su ƙidayuwa! Alhakin zunubaina ya tarar da ni, Har ba na iya gani, Sun fi gashin kaina yawa, na karaya.


“Saboda haka za a misalta Mulkin Sama da wani sarkin da yake so ya yi ƙididdigar dukiyarsa da yake hannun bayinsa.


Da yake ya gagara biya, sai ubangidansa ya yi umarni a sayar da shi da mata tasa da 'ya'yansa da kuma duk abin da ya mallaka, a biya kuɗin.


Ya ba ɗaya talanti biyar, ɗaya talanti biyu, wani kuma ya ba shi ɗaya, kowa dai gwargwadon ƙarfinsa. Sa'an nan ya tafi.


Shi wanda ya karɓi talanti biyar ɗin nan, nan da nan sai ya je ya yi ta jujjuya su, har wuri ya bugi wuri.


Shi wannan da ya karɓi talanti biyar sai ya matso ya kawo waɗansu talanti biyar, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyar, ga shi kuma, na ci ribar biyar.’


Sai mai talanti biyun nan kuma ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyu, ga shi kuma, na ci ribar biyu.’


Shi kuma wanda ya karɓi talanti guda ɗin, sai ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, na sani kai mutum ne mai tsanani, kana son girbi inda ba kai ka shuka ba, mai son banza ne.


Ko kuwa goma sha takwas ɗin nan da hasumiya ta faɗo a kansu, a Siluwam, ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?


Sai ya kira mabartan maigidansa da ɗaya ɗaya, ya ce wa na farko, ‘Nawa maigida yake bin ka?’


Ya kuma ce wa wani, ‘Kai fa, nawa ake binka?’ Sai ya ce, ‘Buhu ɗari na alkama.’ Ya ce masa, ‘Ga takardarka, ka rubuta tamanin.’


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan