2 Sai ya kira wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu,
2 Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu.
Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka naɗa ni sarki, a matsayin Dawuda, tsohona, ko da yake ni yaro ne ƙarami, ban ƙware ba.
Amma Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ce kai yaro ne, Kai dai ka tafi wurin mutanen da zan aike ka,
A lokacin nan almajirai suka zo wurin Yesu, suka ce, “Wa ya fi girma duka a Mulkin Sama?”
ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in ba kun juyo kun zama kamar ƙananan yara ba, har abada ba za ku shiga Mulkin Sama ba.