Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 18:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Har wa yau dai ina gaya muku, in mutum biyu daga cikinku, ra'ayinsu ya zo ɗaya a nan duniya a kan wani abin da za su roƙa, Ubana kuwa da yake Sama zai yi musu shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 “Har wa yau, ina gaya muku cewa in mutum biyu a cikinku a duniya suka yarda su roƙi wani abu, Ubana da yake cikin sama zai yi muku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 18:19
20 Iomraidhean Croise  

Kome kuka roƙa da addu'a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.”


sai ka dakatar da sadakarka a gaban bagadin hadaya tukuna, ka je ku shirya da ɗan'uwanka, sa'an nan ka zo ka miƙa sadakarka.


“Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.


Don haka ina dai gaya muku, kome kuka roƙa da addu'a, ku gaskata cewa samamme ne, za ku kuwa samu.


Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku.


In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku.


A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana.


Duk waɗannan da nufi ɗaya suka nace da addu'a, tare da mata, da Maryamu uwar Yesu, da kuma 'yan'uwansa.


Sai aka tsare Bitrus a kurkuku, Ikkilisiya kuwa ta himmantu ga roƙon Allah saboda shi.


Da kuwa ya ga wahayin, nan take sai muka nemi tafiya Makidoniya, muka tabbata cewa Allah ne ya kira mu mu yi musu bishara.


Mu kuwa sai mu nace da yin addu'a da kuma koyar da Maganar.”


Domin na san duk wannan zai zama sanadin lafiyata, ta wurin addu'arku da taimakon Ruhun Yesu Almasihu.


Mukan kuma sami duk abin da muka roƙa a gare shi, domin muna bin umarninsa, muna kuma yin abin da yake so.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan