Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 18:15 - Littafi Mai Tsarki

15 “In ɗan'uwanka ya yi maka laifi, sai ka je, ka gaya masa laifinsa, kai da shi, ku kaɗai. In ya saurare ka, to, kā maido da ɗan'uwanka ke nan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 18:15
21 Iomraidhean Croise  

Nagarin mutum ya iya hukunta ni, ya tsauta mini da alheri, Zai zamar mini kamar an shafe kaina da mai, Domin kullayaumi ina addu'a gāba da mugayen ayyuka.


Adalci yana rayar da mutum, wanda yake da hikima kuma yakan ceci rayuka.


“Kada wani ya riƙe ɗan'uwansa da ƙiyayya a zuciyarsa, amma ya daidaita rashin jituwa da shi, don kada ya yi zunubi saboda shi.


Haka ma, ba nufin Ubanku da yake cikin Sama ba ne ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya hallaka.”


Sai Bitrus ya matso ya ce masa, “Ya Ubangiji, sau nawa ɗan'uwana zai yi mini laifi in yafe masa? Har sau bakwai?”


Haka kuma Ubana da yake Sama zai yi da ko wannenku, in ba ku yafe wa 'yan'uwanku da zuciya ɗaya ba.”


Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.


Ta haka ne kuke yi wa Almasihu laifi, wato ta wurin yi wa 'yan'uwanku laifi, kuna rushe rarraunan lamirinsu.


To, ko da yake na rubuto muku wasiƙa, ba musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutar ba, sai dai domin a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da kuke yi mana.


Ya ku 'yan'uwa, in an kama mutum yana a cikin yin laifi, ku da kuke na ruhu, sai ku komo da shi a kan hanya da tawali'u, kowa yana kula da kansa kada shi ma ya burmu.


kuna jure wa juna, in kuma wani yana da ƙara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe.


A cikin wannan al'amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan'uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri.


Amma kada ku ɗauke shi a kan abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a kan shi ɗan'uwa ne.


Mutumin da yake sa tsattsaguwa kuwa, in ya ƙi kula da gargaɗinka na farko da na biyu, to, sai ka fita sha'aninsa.


Haka kuma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu, ba tare da wata magana ba,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan