Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 18:13 - Littafi Mai Tsarki

13 In kuwa ya samo ta, labudda, ina gaya muku, ai, farin cikin da yake yi a kanta ya fi na tasa'in da taran nan da ba su taɓa ɓăcewa ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 In kuwa ya same ta, ina gaya muku gaskiya, zai yi murna saboda ɗayan fiye da tasa’in da taran da ba su ɓace ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 18:13
14 Iomraidhean Croise  

Amma yana jin daɗin waɗanda suke tsoronsa, Yana jin daɗin waɗanda suke dogara da madawwamiyar ƙaunarsa.


Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu.


Ubangiji zai ɗauke ki amaryarsa, Za ku yi murna tare, Kamar murnar amarya da ango.


Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ba ku warkar da marasa lafiya ba, ba ku ɗora karayyu ba, waɗanda kuma suka yi makuwa ba ku komar da su ba, waɗanda suka ɓace ba ku nemo su ba, amma kuka mallake su ƙarfi da yaji.


Akwai wani Allah kamarka, mai yafe mugunta, Mai kawar da laifin ringin gādonsa? Ba ya riƙon fushi har abada, gama shi mai alheri ne.


Ubangiji Allahnki yana tsakiyarki, Mayaƙi mai cin nasara ne. Zai yi murna, ya yi farin ciki da ke. Zai sabunta ki da ƙaunarsa. Zai kuma yi murna da ke ta wurin raira waƙa da ƙarfi.


To, me kuka gani? In wani na da tumaki ɗari, ɗayarsu ta băce, ashe, ba zai bar tasa'in da taran nan a gindin dutse, ya je neman wadda ta ɓăce ba?


Haka ma, ba nufin Ubanku da yake cikin Sama ba ne ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya hallaka.”


Ƙauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya.


Gama Shari'a marar jinƙai ce ga wanda ba ya nuna jinƙai. Amma jinƙai yana rinjayar hukunci.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan