Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 18:12 - Littafi Mai Tsarki

12 To, me kuka gani? In wani na da tumaki ɗari, ɗayarsu ta băce, ashe, ba zai bar tasa'in da taran nan a gindin dutse, ya je neman wadda ta ɓăce ba?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 “Me kuka gani? In wani yana da tumaki ɗari, sai ɗaya daga cikinsu ta ɓace, ba sai yă bar tasa’in da taran a kan tuddai yă je neman guda ɗayan da ta ɓace ba?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 18:12
17 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya Batishbe,


Ina kai da kawowa kamar ɓatacciyar tunkiya, Ka zo ka neme ni, ni bawanka, Saboda ban ƙi kulawa da dokokinka ba.


Dukanmu muna kama da tumakin da suka ɓata, Ko wannenmu ya kama hanyarsa. Sai Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa, Hukuncin da ya wajaba a kanmu.


“Mutanena sun zama kamar ɓatattun tumaki, Waɗanda makiyayansu suka bauɗar da su, Suka ɓata a cikin tsaunuka, Suna kai da kawowa daga wannan dutse zuwa wancan. Sun manta da shingensu.


Kamar yadda makiyayi yakan nemo tumakin da suka watse daga cikin garkensa, haka zan nemi tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu.


“Zan nemo ɓatattu, in komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗora karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafan makiyayan nan masu taiɓa, zan hukunta su.


Ba za su ƙara zama ganimar al'ummai ba, namomin jejin ƙasar kuma ba za su cinye su ba. Za su yi zamansu lafiya, ba wanda zai tsorata su.


Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ba ku warkar da marasa lafiya ba, ba ku ɗora karayyu ba, waɗanda kuma suka yi makuwa ba ku komar da su ba, waɗanda suka ɓace ba ku nemo su ba, amma kuka mallake su ƙarfi da yaji.


Tumakina sun watse, suna yawo a kan dukan duwatsu da tuddai, sun warwatsu a duniya duka, ba wanda zai nemo su.’


Ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da tunkiya, ta faɗa a rami ran Asabar, ba zai kama ta ya fitar da ita ba?


In kuwa ya samo ta, labudda, ina gaya muku, ai, farin cikin da yake yi a kanta ya fi na tasa'in da taran nan da ba su taɓa ɓăcewa ba.


“To, me kuka gani? An yi wani mutun mai 'ya'ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’


ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.”


Ina magana da ku a kan ku mahankalta ne fa, ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa.


A dā kun ɓăce kamar tumaki, amma a yanzu kun dawo ga Makiyayi, wato mai kula da rayukanku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan