Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 18:11 - Littafi Mai Tsarki

11 [Domin Ɗan Mutum ya zo ne musamman ceton abin da ya ɓata.]

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 18:11
12 Iomraidhean Croise  

Sai dai ku je wurin batattun tumakin jama'ar Isra'ila, Irm


Ya amsa ya ce, “Ni wurin ɓatattun tumakin jama'ar Isra'ila kaɗai aka aiko ni.”


To, me kuka gani? In wani na da tumaki ɗari, ɗayarsu ta băce, ashe, ba zai bar tasa'in da taran nan a gindin dutse, ya je neman wadda ta ɓăce ba?


Amma da Yesu ya ji haka ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya.


Don ɗan nan nawa dā ya mutu ne, amma a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma a yanzu an same shi.’ Sai suka yi ta farin ciki.


Ai kuwa, daidai ne a yi ta murna da farin ciki, don ɗan'uwan nan naka dā ya mutu, a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma an same shi.’ ”


Don Ɗan Mutum ya zo ne musamman garin neman abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”


Sai suka ci gaba, suka tafi wani ƙauye.


Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace.


Kowa ya ji maganata, bai kuwa kiyaye ta ba, ba ni nake hukunta shi ba. Gama ba don yi wa duniya hukunci na zo ba, sai dai domin in ceci duniya.


Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.


Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum cewa, “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” ni ne kuwa babbansu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan