8 Da suka ɗaga kai ba su ga kowa ba, sai Yesu kaɗai.
8 Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.
Sai Yesu ya zo ya taɓa su, ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”
Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”
Farat haka da suka dudduba, ba su ƙara ganin kowa ba, sai Yesu kaɗai tare da su.
Bayan muryar ta yi magana, aka ga Yesu shi kaɗai. Suka yi shiru. A kwanakin nan kuwa ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.