7 Sai Yesu ya zo ya taɓa su, ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”
7 Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”
Sai hannu ya taɓa ni, ya tashe ni, sa'an nan hannuwana da gwiwoyina suna ta kaɗuwa.
Mai kamannin mutum ɗin nan kuma ya sake taɓa ni, ya kuma ƙarfafa ni.
Sa'ad da yake magana da ni, sai barci mai nauyi ya kwashe ni da nake kwance rubda ciki, amma sai ya taɓa ni, ya tashe ni tsaye.
Sa'ad da nake yin addu'a, sai mutumin nan Jibra'ilu, wanda na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina a gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta maraice.
Sai nan da nan ya yi musu magana ya ce, “Ba kome, Ni ne, kada ku ji tsoro.”
Da almajiran suka ji haka, sai suka faɗi ƙasa, tsoro ya kama su.
Da suka ɗaga kai ba su ga kowa ba, sai Yesu kaɗai.
Don tsoro, matan suka sunkuyar da kansu ƙasa. Mutanen suka ce musu, “Don me kuke neman rayayye a cikin matattu?
Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”
Da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa kamar na mutu. Amma ya ɗora mini hannunsa na dama, ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne na Farko. Ni ne na Ƙarshe,