Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 17:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 17:5
38 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya yi magana da Ayuba ta cikin guguwa.


Sa'ad da kuke shan wahala Kuka yi kira a gare ni, na kuwa cece ku. Daga maɓuyata cikin hadiri, na amsa muku, Na jarraba ku a maɓuɓɓugan Meriba.


Da busar ƙaho ta ƙara tsananta, sai Musa ya yi magana, Ubangiji kuwa ya amsa masa da tsawa.


Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.


Ubangiji shi Allah ne da ya ƙosa ya yi ceto saboda gaskiyarsa, Saboda haka yana so a girmama koyarwarsa,


“Ga barana wanda na zaɓa! Ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Zan sa masa Ruhuna, zai kuma sanar da al'ummai hanyar gaskiya.


Da almajiran suka ji haka, sai suka faɗi ƙasa, tsoro ya kama su.


Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai.”


Aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai.”


Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena. Ku saurare shi.”


Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa da wata kama, kamar kurciya. Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai,”


“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.


Uban yana ƙaunar Ɗan, ya kuma sa kome a hannunsa.


Uban kuma da ya aiko ni, shi kansa ya shaide ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ba, ko ganin kama tasa.


Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi Sama, wani gajimare ya tafi da shi, ba su ƙara ganinsa ba.


Wannan shi ne Musan da ya ce wa Isra'ilawa, ‘Allah zai tasar muku da wani annabi daga cikin 'yan'uwanku, kamar yadda ya tashe ni.’


domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa.


“Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamata daga cikin jama'arku, sai ku saurare shi.


Duk wanda bai saurari maganata wadda zai faɗa da sunana ba, ni da kaina zan nemi hakkinta a gare shi.


“Ubangiji ya faɗa wa taron jama'arku waɗannan dokoki da murya mai ƙarfi ta tsakiyar wuta, da girgije, da duhu baƙi ƙirin. Ya rubuta su a bisa alluna biyu na dutse, ya ba ni, ba abin da ya ƙara.”


Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa,


da ya kai ga kammala, sai ya zama tushen madawwamin ceto ga dukkan waɗanda suke masa biyayya,


Ga shi, zai zo a cikin gajimare, kowa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka a kansa. Wannan haka yake. Amin.


Sa'an nan na duba, sai ga wani farin gajimare, da wani kamar Ɗan Mutum a zaune a kan gajimaren, da kambin zinariya a kansa, da kakkaifan lauje a hannunsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan