Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 17:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin. In kana so, sai in kafa bukkoki uku a nan, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 17:4
16 Iomraidhean Croise  

Za ka nuna mini hanyar rai, Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki, Taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada.


Akwai mutane da yawa da suke cewa, “Da ma a sa mana albarka!” Ka dube mu da alheri, ya Ubangiji!


Wata rana za ku ga sarki mai ɗaukaka yana mulki a dukan ƙasar da take shimfiɗe zuwa kowace kusurwa.


Wane irin kyau da bansha'awa alherinsa yake! Hatsi zai sa samari su yi murna. Sabon ruwan inabi kuma zai sa 'yan mata su yi farin ciki.


Ga shi, Musa da Iliya sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu.


Mutanen nan na rabuwa da shi ke nan, sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Maigida, ya kyautu da muke nan wurin. Mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” Bai ma san abin da yake faɗa ba.


Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba.


Idin Bukkoki na Yahudawa kuwa ya gabato.


Duka biyu suna jan hankalina ƙwarai. Burina in ƙaura in zauna tare da Almasihu, domin wannan shi ne ya fi kyau nesa.


Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.


Birnin kuwa ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, domin ɗaukakar Allah ita ce haskensa, Ɗan Ragon kuma fitilarsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan