Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 17:23 - Littafi Mai Tsarki

23 za su kuwa kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Sai duk tsananin baƙin ciki ya rufe su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Za su kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Almajiran kuwa suka cika da baƙin ciki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 17:23
18 Iomraidhean Croise  

Saboda ba za ka yarda in shiga lahira ba, Ba za ka bar wanda kake ƙauna a zurfafa daga ƙarƙas ba.


Maƙogwarona ya bushe kamar ƙura, Harshena kuma na liƙe wa dasashina na sama. Ka bar ni matacce cikin ƙura.


Aka ƙware shi ba tausayi, Amma ya karɓa da tawali'u, Bai ko ce uffan ba. Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa, Kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya, Bai ko ce uffan ba.


Za ta kasance har shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, sa'an nan za a kashe Masihan, ba zai sami kome ba. Jama'ar shugaban da zai zo za su hallaka birnin da Haikali. A ƙarshensa za a yi rigyawa, da yaƙe-yaƙe, da hallakarwa kamar yadda aka ƙaddara.


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.


Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”


su bashe shi ga al'ummai, su yi masa ba'a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.”


suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu.


Ya fara koya musu, cewa lalle ne Ɗan Mutum ya sha wuya iri iri, shugabanni, da manyan firistoci, da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi da rai.


Sai suka tashi daga nan, suka ratsa ƙasar Galili, bai kuwa so kowa ya sani ba,


Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙin ciki ya cika zuciyarku.


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe Haikalin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan