Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 17:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Tun suna ƙasar Galili, sai Yesu ya ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Da suka taru a Galili, sai ya ce musu, “Za a bashe Ɗan Mutum, a hannun mutane.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 17:22
21 Iomraidhean Croise  

Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.


Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin Mulkinsa.”


Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa san shi ne ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗan Mutum zai sha wuya a hannunsu.”


za su kuwa kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Sai duk tsananin baƙin ciki ya rufe su.


Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”


A sa'an nan da yawa za su yi tuntuɓe, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna.


Tun daga lokacin nan ne ya riƙa neman hanyar da zai bashe shi.


Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe ni nan, ya matso!”


Ya fara koya musu, cewa lalle ne Ɗan Mutum ya sha wuya iri iri, shugabanni, da manyan firistoci, da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi da rai.


Ashe, ba wajibi ne Almasihu ya sha wuyar waɗannan abubuwa ba, ya kuma shiga ɗaukakarsa?”


ya kuma ce musu, “Haka yake a rubuce, cewa wajibi ne Almasihu ya sha wuya, a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu,


Ya ce, “Lalle ne Ɗan mutum yă sha wuya iri iri, shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.”


Duk aka yi mamakin girman ikon Allah. Tun dukansu suna mamakin duk abubuwan da yake yi, sai ya ce wa almajiransa,


A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa,


Abin nan kuwa da na karɓa a gun Ubangiji, shi ne na ba ku, cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki gurasa,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan