Sa'an nan ya yi addu'a da gaske ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, don me ka kawo wa gwauruwan nan da nake zaune wurinta masifa, ka aukar wa ɗanta da ajali?”
Sai na mai da hankalina wajen Ubangiji Allah, ina nemansa ta wurin addu'a, da roƙe-roƙe tare da azumi, ina saye da tufafin makoki, na zauna cikin toka.
Daga nan ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa. Haka zai zamar wa wannan mugun zamani.”
Kada ɗayanku yă ƙaurace wa ɗaya, sai ko da yardar juna zuwa wani ɗan lokaci kaza, don ku himmantu ga addu'a, sa'an nan ku sāke haɗuwa, kada Shaiɗan yă zuga ku ta wajen rashin kamewa.
a koyaushe kuna addu'a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu'a.