Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 17:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 17:17
25 Iomraidhean Croise  

A shekara arba'in ɗin nan, Jama'ar nan ta zama abar ƙyama gare ni, ‘Su marasa biyayya ne,’ in ji ni, ‘Gama sun ƙi bin umarnaina!’


Saboda haka Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi yarda ka ba da kanka a gare ni? Saki jama'ata don su tafi su yi mini sujada.


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe za ku ƙi kiyaye dokokina da umarnaina?


Ta ce, “Wawayen mutane! Har yaushe za ku yi ta kasancewa haka? Har yaushe za ku daina jin daɗin yi wa mai ilimi ba'a? Faufau ba za ku taɓa koya ba?


Har yaushe rago zai yi ta ɓalɓalcewa? Yaushe zai farka?


Ubangiji ne ya sa su ba da gurguwar shawara. Sakamakon haka sai Masar ta yi ta aikata dukan abu a hugunce, tana tangaɗi kamar bugagge wanda santsi na kwasarsa cikin aman da ya yi.


Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki, Domin a cece ki, Har yaushe mugayen tunaninki za su yi ta zama a cikinki?


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe mutanen nan za su raina ni? Har yaushe za su ƙi gaskata ni, ko da yake na aikata alamu a tsakiyarsu?


“Har yaushe wannan mugun taron jama'a zai yi ta gunaguni a kaina? Na ji gunagunin da Isra'ilawa suka yi a kaina.


Bai kuma yi mu'ujizai masu yawa a can ba, saboda rashin bangaskiyarsu.


Da Yesu ya lura da haka sai ya ce, “Ya ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da juna a kan ba ku zo da gurasa ba?


Na kuwa kai shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”


Sai Yesu ya tsawata masa, aljanin kuma ya rabu da shi. Nan take yaron ya warke.


To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!


Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa'an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit!


Daga baya ya bayyana ga sha ɗayan nan, su kansu, sa'ad da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurinkansu, domin ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi ba.


Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ya ku mutanen zamani marar bangaskiya! Har yaushe zan iya zama da ku? Har yaushe kuma zan iya jure muku? Ku dai kawo mini shi.”


Sai Yesu ya ce musu, “Ya ku mutane marasa fahimta, masu nauyin gaskata duk abin da annabawa suka faɗa!


Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku tsara marasa bangaskiya, kangararru! Har yaushe zan zama da ku, ina jure muku? Kawo ɗa naka nan.”


Sa'an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsanka nan, ka ji hannuwana. Miƙo hannunka kuma ka sa a kwiɓina. Kada ka zama marar ba da gaskiya, sai dai mai ba da gaskiya.”


Wajen shekara arba'in yake haƙuri da su cikin jeji.


Sai ya yi ta tabbatar musu da maganganu masu yawa, yana ta yi musu gargaɗi, yana cewa, “Ku tsirar da kanku daga wannan karkataccen zamani.”


Da ma a ce ku jure 'yar wautata. Ku dai yi haƙuri da ni!


Sun aikata mugunta a gabansa, Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu, Su muguwar tsara ce, karkatacciya,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan