Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.”
To, sunansa ne, wato ta wurin bangaskiya ga sunansa, shi ne ya ba mutumin nan da kuke gani, kuka kuma sani, ƙarfi. Hakika, bangaskiyar da take ta wurin Yesu ita ta ba mutumin nan cikakkiyar lafiya, a gaban idonku duka.