Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 17:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa san shi ne ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗan Mutum zai sha wuya a hannunsu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 17:12
25 Iomraidhean Croise  

To, da Yahaya ya ji a kurkuku labarin ayyukan Almasihu, sai ya aiki almajiransa,


Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.


Ya amsa ya ce, “Lalle Iliya zai zo ne, zai kuwa raya dukan abubuwa.


Sa'an nan ne almajiran suka gane, ashe, zancen Yahaya Maibaftisma yake yi musu.


Tun suna ƙasar Galili, sai Yesu ya ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane,


Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”


Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”


Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da sheƙunan, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”


“Ga shi, Yahaya Maibaftisma ya zo, ba ya cin gurasa, ba ya shan ruwan inabi, amma kuna cewa, ‘Ai, yana da iska.’


Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba.


shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi.


to, sai ku sani, ku duka, da kuma duk jama'ar Isra'ila, da sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda ku kuka gicciye, wanda kuma Allah ya tashi shi daga matattu, albarkacinsa ne mutumin nan yake tsaye a gabanku lafiyayye.


A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan