11 Ya amsa ya ce, “Lalle Iliya zai zo ne, zai kuwa raya dukan abubuwa.
11 Yesu ya amsa ya ce, “Tabbatacce, Iliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa.
Zai sāke kawo iyaye da 'ya'ya wuri ɗaya, da ba don haka ba, da sai in zo in hallaka ƙasar.”
Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, yaya malaman Attaura suke cewa, lalle ne Iliya ya riga zuwa?”
Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa san shi ne ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗan Mutum zai sha wuya a hannunsu.”
Saboda haka da suka taru, suka tambaye shi suka ce, “Ya Ubangiji, yanzu ne za ka sāke kafa wa Isra'ila mulki?”
wanda lalle ne ya zauna a Sama, har kafin lokacin nan na sabunta dukkan abubuwa da Allah ya faɗa tun zamanin dā ta bakin annabawansa tsarkaka.