Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 16:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sai Yesu ya ce musu, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Yesu ya ce musu, “Ku yi hankali, ku yi taka zallan da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 16:6
15 Iomraidhean Croise  

A kowace hadaya ta gari da za a kawo wa Ubangiji, ba za a sa yisti ba, gama ba za a yi hadayar ƙonawa ga Ubangiji da yisti, ko da zuma ba.


Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo suka roƙe shi ya nuna musu wata alama daga Sama, domin su gwada shi.


Yaya kuka kasa ganewa? Ba zancen gurasa na yi ba, sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”


Sa'an nan ne fa suka fahimta cewa, ba ce musu ya yi, su yi hankali da yistin gurasa ba, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da ta Sadukiyawa.


Da almajiran suka isa wancan ƙetare, ashe, sun manta ba su kawo gurasa ba.


Sai suka yi magana da juna suka ce, “Ba mu kawo gurasa ba fa!”


Amma da Yahaya ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa, sun taho domin a yi musu baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?


Ya gargaɗe su ya ce, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Hirudus.”


Sa'an nan kuwa da dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, da farko ya yi magana da almajiransa. Ya fara cewa, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, makirci.


Ya kuma ce musu, “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne rai ba.”


Almajiran suka ce wa juna, “Shin, wani ya kawo masa abinci ne?”


Ai, ɗan yisti kaɗan, yake game dukkan curin gurasa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan