5 Da almajiran suka isa wancan ƙetare, ashe, sun manta ba su kawo gurasa ba.
5 Da suka ƙetare tafkin, almajiran sun manta su riƙe burodi.
Da ya sallami taron ya shiga jirgi ya tafi ƙasar Magadan.
'Yan zamani, mugaye, maciya amana, suke nema su ga wata alama, amma ba wata alamar da za a nuna musu, sai dai ta Yunusa.” Sai ya bar su ya tafi.
Sai Yesu ya ce musu, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”