Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 16:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 16:25
10 Iomraidhean Croise  

Gama idan kin yi shiru a irin wannan lokaci, to, taimako da ceto za su zo wa Yahudawa ta wata hanya dabam, amma ke da gidan iyayenki za ku halaka. Wa ya sani ko saboda irin wannan lokaci ne kika sami wannan maƙami?”


“Ka tattara dukan Yahudawan da suke a Shushan, su yi domin, kada su ci ko su sha dare da rana, har kwana uku. Ni kuma da kuyangina za mu yi haka nan. Sa'an nan zan tafi wurin sarki, ko da yake ba bisa ga doka ba, idan na halaka, na halaka ke nan.”


Shi ne kuma yake sa lokacin nema, da lokacin rashi, Da lokacin adanawa, da lokacin zubarwa,


Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, adana shi yake yi.”


Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?


Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, saboda bishara kuma, tattalinsa ya yi.


Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa, adana shi ya yi.


Mai ƙaunar ransa zai rasa shi. Wanda kuwa ya ƙi ransa a duniyan nan, ya kiyaye shi ke nan, har ya zuwa rai madawwami.


Sun kuwa yi nasara da shi albarkacin jinin Ɗan Ragon nan, da kuma albarkacin maganar da suka shaida, domin ba su yi tattalin ransu ba, har abin ya kai su ga kisa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan