Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 16:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya bi ni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 16:24
18 Iomraidhean Croise  

Wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba.


Suna tafiya ke nan, sai suka gamu da wani Bakurane, mai suna Saminu. Shi ne suka tilasta wa ya ɗauki gicciyen Yesu.


Yesu ya dube shi duban ƙauna, ya ce masa, “Abu guda ne kawai ya rage maka. Sai ka je, ka sayar da duk mallakarka, ka ba gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”


Sai ga wani mai wucewa, wai shi Saminu Bakurane, uban Iskandari da Rufas, yana zuwa daga ƙauye. Suka fa tilasta masa ya ɗauki gicciyen Yesu.


Ya kira taron tare da almajiransa, ya ce musu, “Duk mai son bina, sai yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.


Duk wanda bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.


Suna tafiya da Yesu yake nan, sai suka cafke wani, mai suna Saminu Bakurane, yana zuwa daga ƙauye, suka ɗora masa gicciye, yă ɗauka ya bi Yesu.


Sai suka tafi da Yesu. Ya kuwa fita, shi kansa yake ɗauke da gicciyensa, har zuwa wurin da ake kira Wurin Ƙoƙon Kai, da Yahudanci kuwa, Golgota.


(Ya faɗi wannan ne yana kwatanta irin mutuwar da Bitrus zai yi ya ɗaukaka Allah.) Bayan ya faɗi haka, ya ce masa, “Bi ni.”


Yesu ya ce masa, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki? Kai dai, bi ni!”


suna ƙarfafa masu bi, suna yi musu gargaɗi su tsaya ga bangaskiya, suna cewa, sai da shan wuya mai yawa za mu shiga Mulkin Allah.


To, a yanzu ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, a jikina kuma ina cikasa abin da ya saura ga wahalar Almasihu, da aka aza mini saboda jikinsa, wato Ikilisiya,


don kada kowa ya raurawa a cikin tsananin wahalar nan. Ai, ku kanku kun sani an nufe mu da haka ne.


Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna ga Almasihu Yesu, za su sha tsanani.


Domin a kan haka ne musamman aka kira ku. Gama Almasihu ma ya sha wuya dominku, ya bar muku gurbi ku bi hanyarsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan