Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 16:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka yi nesa da ni, ya Shaiɗan! Tarko kake a gare ni. Ba ka tattalin al'amuran Allah, sai dai na mutane.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin al’amuran Allah, sai dai al’amuran mutane.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 16:23
19 Iomraidhean Croise  

Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga 'ya'yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la'antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.


Amma Dawuda ya ce wa Abishai da ɗan'uwansa Yowab, “Ina ruwana da ku, ku 'ya'yan Zeruya? Kuna so ku jawo mini wahala? Ni ne Sarkin Isra'ila yanzu, don haka ba Ba'isra'ilen da za a kashe a yau.”


Shaiɗan ya tashi gaba da Isra'ila, sai ya iza Dawuda ya ƙidaya Isra'ilawa.


Saboda tsananin tsarkina na zama kamar dutse wanda mutane suke tuntuɓe da shi. Na zama kamar tarko wanda zai kama jama'ar mulkokin Yahuza da Isra'ila da mutanen Urushalima.


Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawata masa, ya ce, “Allah ya sawwaƙe, ya Ubangiji! Wannan har abada ba zai same ka ba!”


“Kaiton duniya saboda sanadodin tuntuɓe! Lalle sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadin!


Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa, ‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”


Amma da Yesu ya waiwaya ya ga almajiransa, ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Ka yi nesa da ni, Shaiɗan! Ba ka tattalin al'amuran Allah sai na mutane.”


Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake cewa, “ ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”


Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba ni na zaɓe ku, ku goma sha biyu ba? To, ɗayanku Iblis ne.”


Saboda haka kada mu ƙara ganin laifin juna, gara mu ƙudura, don kada kowannenmu yă zama sanadin tuntuɓe ko faɗuwa ga ɗan'uwansa,


Ya kyautu kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa ɗan'uwanku yin tuntuɓe.


Ƙarshensu hallaka ne, Allahnsu ciki ne, rashin kunyarsu ita ce abar taƙamarsu, sun ƙwallafa ransu a kan al'amuran duniya.


Ku ƙwallafa ranku a kan abubuwan da suke Sama, ba a kan abubuwan da suke a ƙasa ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan