Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 16:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 16:21
31 Iomraidhean Croise  

Wato, kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗan Mutum zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa.


Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawata masa, ya ce, “Allah ya sawwaƙe, ya Ubangiji! Wannan har abada ba zai same ka ba!”


Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin Mulkinsa.”


Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa san shi ne ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗan Mutum zai sha wuya a hannunsu.”


Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”


kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba sai dai domin shi ya yi bautar, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”


“Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi.”


Kafin ya rufe baki ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci da shugabanni ne suka turo su.


Amma da manyan firistoci da shugabanni suka kai ƙararrakinsa, bai ce kome ba.


suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu.


Ai, ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da aka sa shi.


Ya fara koya musu, cewa lalle ne Ɗan Mutum ya sha wuya iri iri, shugabanni, da manyan firistoci, da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi da rai.


Sai ya ce musu, “Lalle ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwa. Yaya kuwa yake a rubuce a kan Ɗan Mutum, cewa zai sha wuya iri iri, a kuma wulaƙanta shi?


Amma lalle sai ya sha wuya iri iri tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ƙi shi.


ya kuma ce musu, “Haka yake a rubuce, cewa wajibi ne Almasihu ya sha wuya, a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu,


Sun bayyana da ɗaukaka, suna zancen ƙaura tasa ne, wadda yake gabannin yi a Urushalima.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan