Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 16:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Zan ba ka mabuɗan Mulkin Sama. Kome ka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome ka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 16:19
14 Iomraidhean Croise  

Zan sa shi ya zama sarki mai cikakken iko, na zuriyar Dawuda. Mabuɗan fāda suna hannunsa, abin da ya buɗe, ba mai ikon rufewa. Abin da ya rufe kuwa ba mai ikon buɗewa.


“Hakika, ina gaya muku, kome kuka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome kuka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne.


Duk waɗanda kuka gafarta wa zunubansu, an gafarta musu ke nan. Duk waɗanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta ba ke nan.”


Bayan an yi ta muhawwara da gaske, Bitrus ya miƙe, ya ce musu, “Ya 'yan'uwa, kun sani tun farkon al'amari, Allah ya yi zaɓe a cikinku, cewa dai ta bakina ne al'ummai za su ji maganar bishara, su ba da gaskiya.


Wanda kuka yafe wa kome, ni ma na yafe masa. Abin da na yafe kuwa, in dai har ma akwai abin yafewa, saboda ku ne na yafe masa, albarkacin Almasihu,


Saboda haka, kowa ya ƙi yarda da wannan, ba mutum ya ƙi ba, amma Allah ya ƙi, shi da yake ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.


ni ne kuma Rayayye. Dā na mutu, amma ga shi a yanzu, ina a raye har abada abadin, ina kuwa da mabuɗan mutuwa da na Hades.


Suna da ikon hana ruwan sama, don kada a yi ruwa a duk kwanakin da suke yin annabci, suna kuma da iko a kan ruwa, su mai da shi jini, su kuma ɗora wa duniya kowane irin bala'i, a duk lokacin da suke so.


“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Filadalfiya haka, ‘Ga maganar Mai Tsarkin nan, Mai gaskiya, wanda yake da mabuɗin Dawuda, wanda in ya buɗe, ba mai rufewa, in kuma ya rufe, ba mai buɗewa.


Mala'ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga wani tauraron da ya faɗa a kan duniya daga sama, aka ba shi mabuɗin ramin mahallaka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan