Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 16:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, a kan dutsen nan ne zan gina ikilisiyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ta ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hades ba za su rinjaye ta ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 16:18
42 Iomraidhean Croise  

hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,


Sai sarki ya ce musu, “Duk abin da kuka ga ya fi muku kyau, shi zan yi.” Sarki kuwa ya tsaya a bakin ƙofar garin sa'ad da sojojin suke fita, kashi kashi, ɗari ɗari, da dubu dubu.


An taɓa nuna maka ƙofofin mutuwa? Ko kuwa ka taɓa ganin ƙofofin duhu ƙirin?


Ba su so su ga abinci, Sun kusa mutuwa.


Mai farin ciki ne mutumin da yake da irin waɗannan kibau da yawa! Faufau ba za a ci nasara a kansa ba, Sa'ad da ya kara da maƙiyansa a wurin shari'a.


“Maƙiyana suka tsananta mini da mugunta, Tun ina ƙarami, Amma ba su yi nasara da ni ba.


A tituna suna ta magana a kaina, Bugaggu da giya kuwa suna raira waƙa a kaina.


Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai! Ka dubi irin wulakancin da maƙiya suka yi mini! Ka kuɓutar da ni daga mutuwa, ya Ubangiji,


Kalmomi masu hikima sun yi wa wawa zurfin ganewa ƙwarai, ba shi da ta cewa sa'ad da ake magana a kan muhimman abubuwa.


Yanzu fa ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan kafa ƙaƙƙarfan harsashin gini a Sihiyona. A kansa zan sa ƙaƙƙarfan dutsen kusurwa. A kansa an rubuta wannan magana, ‘Amincin da yake kafaffe mai haƙuri ne kuma.’


Zai ba da ruhun adalci ga waɗanda suke alƙalai, ƙarfin hali kuma ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofin birni.


Na zaci a gaɓar ƙarfina Zan tafi lahira, Ba zan ƙara rayuwa ba.


Amma ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki, Za ki iya amsa wa dukan waɗanda za su yi ƙararki. Zan kāre bayina, In kuwa ba su nasara.” Ubangiji ne ya faɗa.


Na tafi can ƙasa ƙarƙashin tussan duwatsu. Ƙasar da ƙofarta take rufe har abada, Amma ka fitar da ni daga cikin ramin, ya Ubangiji Allahna.


To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya,


Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi, har Hades. Da mu'ujizan da aka yi a cikinki, su aka yi a Saduma, da ta wanzu har ya zuwa yau.


In kuma ya ƙi sauraronsu, sai ka shaida wa ikilisiya. In kuma har ya ƙi sauraron ikilisiyar, ka maishe shi kamar bare, ko mai karɓar haraji.”


Yana tafiya a bakin Tekun Galili ke nan, sai ya ga waɗansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, don su masunta ne.


“Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā.


Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato Bitrus.


suna yabon Allah, suna da farin jini a wurin dukan mutane. Kowace rana kuma Ubangiji yana ƙara masu waɗanda ake ceta.


Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.


Shawulu kuwa yana goyon bayan kisan Istifanas. A ran nan kuwa wani babban tsanani ya auko wa Ikkilisiyar da take Urushalima. Duk aka warwatsa su a lardin Yahudiya da na Samariya, sai dai manzannin kawai.


“Ke mutuwa, ina nasararki? Ke mutuwa, ina ƙarinki?”


sai Yakubu da Kefas da Yahaya, su da suke shahararrun ginshiƙan ikkilisiya, da suka ga alherin da Allah ya yi mini, sai suka karɓe mu, ni da Barnaba, hannu biyu biyu, domin mu mu je wurin al'ummai, su kuwa gun masu kaciya.


An yi wannan ne kuwa domin a yanzu a sanar da hikimar Allah iri iri ga manyan mala'iku da masu iko a samaniya, ta hanyar Ikkilisiya.


Wannan asiri muhimmi ne, ni kuwa ina nufin Almasihu ne da ikkilisiya.


Shi ne kai ga jikin nan, wato Ikilisiya. Shi ne tushe, na farko a cikin masu tashi daga matattu, domin ta wurin kowane abu ya zama shi ne mafifici.


don in ya zamana na yi jinkiri, za ka san irin zaman da ya kamata a yi a jama'ar Allah, wadda take ita ce Ikkilisiyar Allah Rayayye, jigon gaskiya da kuma ginshiƙinta.


Don kuwa in mutum bai san yadda zai sarrafa iyalinsa ba, ta ƙaƙa zai iya kula da ikkilisiyar Allah?


Saboda haka, sai mu yi godiya domin mun sami mulkin da ba ya girgizuwa, ta haka kuma mu yi wa Allah sujada abar karɓa, tare da tsoro da tsananin girmamawa,


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Garun birnin kuwa, tana da dutsen harsashi goma sha biyu, a jikinsu kuma an rubuta sunayen manzannin nan goma sha biyu na Ɗan Ragon.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan