Ina umartar mutanen da suke cikin mulkina su yi rawar jiki, su ji tsoron Allah na Daniyel, “Gama shi Allah ne mai rai, Madawwami, Sarautarsa ba ta tuɓuwa, Mulkinsa kuma madawwami ne.
Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”
“Don me kuke haka? Ai, mu ma 'yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu.
A fili yake, ku wasiƙa ce ta Almasihu, ta hannunmu, ba kuwa rubutun tawada ba ne, amma na Ruhun Allah Rayayye ne, ba kuwa a kan allunan dutse aka rubuta ta ba, sai dai a zuci.
Wace yarjejeniya ce take a tsakanin Haikalin Allah da gumaka? Domin mu haikali ne na Allah Rayayye. Yadda Allah ya ce, “Zan zauna tare da su, in yi yawo a tsakaninsu, Zan kuma kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata.
Domin su da kansu suke ba da labarin irin ziyartarku da muka yi, da kuma yadda kuka rabu da gumaka, kuka juyo ga Allah, domin ku bauta wa Allah Rayayye na gaskiya,
don in ya zamana na yi jinkiri, za ka san irin zaman da ya kamata a yi a jama'ar Allah, wadda take ita ce Ikkilisiyar Allah Rayayye, jigon gaskiya da kuma ginshiƙinta.
Saboda wannan maƙasudi muke wahala, muke ta fama, domin mun dogara ne ga Allah Rayayye, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman masu ba da gaskiya.
balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.
Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.
Sai na ga wani mala'ika yana hawa daga mafitar rana, riƙe da hatimin Allah Rayayye. Sai ya yi wa mala'ikun nan huɗu magana da murya mai ƙarfi, waɗanda aka bai wa ikon azabtar da ƙasa da teku,