Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 16:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Sai suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa Iliya, waɗansu kuma Irmiya, ko kuwa ɗaya daga cikin annabawa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Suka amsa, “Waɗansu suna ce Yohanna Mai Baftisma; waɗansu kuma suna ce annabi Iliya; har wa yau waɗansu suna ce Irmiya ne ko kuma ɗaya daga cikin annabawa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 16:14
14 Iomraidhean Croise  

Maganar Irmiya ɗan Hilkiya ke nan, na cikin firistocin da suke a Anatot, a yankin ƙasar Biliyaminu,


“Ga shi, zan aiko muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji ta zo.


Sai ya ce wa barorinsa, “Wannan, ai, Yahaya Maibaftisma ne, shi aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”


Ya ce musu, “Amma ku fa, wa kuke cewa, nake?”


Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, yaya malaman Attaura suke cewa, lalle ne Iliya ya riga zuwa?”


A wannan zamani ne Yahaya Maibaftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya,


Amma waɗansu kuwa suka ce, “Iliya ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawa.”


Suka ce masa, “Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa, Iliya, waɗansu kuma, wani daga cikin annabawa.”


Waɗansu kuwa suka ce wai Iliya ne ya bayyana. Waɗansu kuma suka ce ɗaya daga annabawan dā ne ya tashi.


Sai suka tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A'a, ba shi ba ne.” Suka ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A'a.”


Taro kuma suka riƙa maganarsa a raɗe, waɗansu na cewa, “Mutum ne nagari.” Waɗansu kuma na cewa, “A'a, ai, ɓad da jama'a yake.”


Sai suka sāke ce wa makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da yake kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai, annabi ne.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan