Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 16:13 - Littafi Mai Tsarki

13 To, da Yesu ya shiga ƙasar Kaisariya Filibi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke cewa, Ɗan Mutum yake?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Sa’ad da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke ce da Ɗan Mutum?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 16:13
23 Iomraidhean Croise  

“A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum. Yana zuwa cikin gizagizai, Ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal, Aka kai shi gabansa.


Kowa ya aibata Ɗan Mutum, ā gafarta masa. Amma wanda ya aibata Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, duniya da lahira.”


Wato, kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗan Mutum zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa.


Domin Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”


Ya amsa ya ce, “Mai yafa kyakkyawan irin nan, shi ne Ɗan Mutum.


Ɗan Mutum zai aiko mala'ikunsa, za su tattaro duk masu sa mutane laifi, da kuma duk masu yin mugun aiki, su fitar da su daga Mulkinsa,


Yesu ya tashi daga nan, ya tafi zuwa ƙasar Taya da Sidon.


Domin Ɗan Mutum zai zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. A sa'an nan ne zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikinsa.


Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin Mulkinsa.”


“Sa'ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala'iku duka, sa'an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa.


Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da sheƙunan, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”


Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya” sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.”


Domin Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”


Duk wanda zai ji kunyar shaida ni da maganata a wannan zamani na rashin amana da yawan zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi, sa'ad da ya zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'iku tsarkaka.”


Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala'ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.”


Sai taron suka amsa masa suka ce, “Shari'armu ta gaya mana, cewa Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?”


Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,


Ya kuma ba shi ikon zartar da hukunci, saboda shi Ɗan Mutum ne.


wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.


Sai ya ce, “Ga shi, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗan Mutum tsaye dama ga Allah.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan